An kashe 'yan tawaye 5 sakamakon rikicin da suka fafata da jami'an tsaron Indiya a yankin Jammu Kashmir.
Jaridar "The Indian Times" ta bayyana cewar bayan bayanan sirri da jami'an tsaro suka samu a yankin Shopian, sun kai farmaki wanda ya sanya aka samu arangama tsakaninsu da 'yan tawaye.
A arangamar da aka yi an kashe 'yan tawaye 5. An yanke sadarwar yanar gizo a yankin bayan arangamar.