An fadakar akan yiwuwar afkuwar mahaukaciyar guguwa a Japan

An fadakar akan yiwuwar afkuwar mahaukaciyar guguwa a Japan

A kasar Japan an yi  gargadi kan yiwuwar afkuwa guguwar Mirinae da Lupit.

Hukumar Kula da Yanayi ta Japan (JMA) ta bayyana cewa guguwar Mirinae, wacce ke tafiya da gudun kilomita 108 a tekun Pacific, za ta shafi Tokyo babban birnin kasar.

JMA ta jaddada cewa guguwar Lupit, wadda ake sa ran za ta rasta daga kudu maso yammacin kasar, za ta kuma shafi lardunan Kyushu.

A cewar kafar yada labarai ta NHK, JMA ta yi kira ga jama'a da su yi taka tsantsan da guguwar da za ta shafi daukacin yankin Kanto-Koshin da lardunan Kyushu, ciki har da Tokyo.

Kananan hukumomi a kasar sun dauki matakan da suka dace don hana hazo mai yawa, ambaliyar kogi da zaftarewar kasa.


News Source:   ()