A sansanin kawancen NATO da ke garin Naples na kasar Italiya, an kama wani sojan Faransa bisa zargin sa da yin leken asiri a madadin Rasha.
Labaran da tashar Europe 1 ta fitar na cewa sojan da ba a bayyana sunansa ba, a lokacin da yake dawowa bakin aikinsa zuwa sansanin NATO na garin Naples a ranar 21 ga Agusta, ya shiga komar jami'an leken asiri na Faransa inda suka fara gudanar da bincike kan zargin yana ba wa Rasha wasu bayanai na sirri da takardu masu mihimmanci mallakar NATO din.
A labarin an bayyana cewar an gurfanar da sojan mai babban mukami da ke da shekaru kusan 50 a gaban kotu bisa zargin sa da "ba wa kasashen waje bayanai, jefa manufofin kasa cikin hatsari da tattara bayana na cutar da kasa".