A Yaman, an bayar da umarnin a kamowa tare da saka takunkumi kan dukiyoyin mambobin Kungiyar Houthi su 175 da suka hada da Shugabanta Abdulmalik Al-Houthi, sakamakon samun su da laifin kokarin kifar da halastacciyar gwamnati da kafa kungiyar 'yan ta'adda.
Kotun soji da ke lardin Ma'arib ta fitar da sanarwar cewa, ta gudanar da zama a karo na 2 na tuhumar mayakan Houthi su 175 da laifin juyin mulki ga halastacciyar gwamnati.
A zaman kotun da lauyan mutanen 175 ya halarta, an bayar da umarnin a kamo tare da sanya takunkumi kan dukiyoyinsu a ciki da wajen Yaman.
Mayakan Houthi ba su fitar da wata sanarwa game da wannan hukunci na kotun ba.
A ranar 7 ga watan Yuli aka yi zama na farko na Shari'ar.
Ofishin gabatar da kara na soji ya zargi Shugaban Houthi da wasu mutane 174 da laifin kafa kungiyar ta'adda ta Ansarullah karkashin kulawar kungiyar Hezbollah ta Labanan da Dakarun Juyin Juya Hali Iran.