An ciro gawarwakin 'yan gudun hijira 25 da suka dilmiye a tekun Yaman

An ciro gawarwakin 'yan gudun hijira 25 da suka dilmiye a tekun Yaman

A gabar tekun garin Lahij na Yaman an ciro jikkunan 'yan kasashen Afirka 'yan gudun hijira su 25 da suka mutu sakamakon kifewar jirgin ruwan da suke ciki.

Ali Yusuf Al-Debash da ke aiki a sansanin 'yan gudun hijirar Afirka na Harez ya shaida cewa, masunta a gabar Lahij da ke tsakanin gundumomin Ras Al-Are da Al-Mudaraba ne suka gano gawarwakin 'yan gudun hijirar.

Debash ya shaida cewa, an ciro gawarwakin mutanen su 25 da jirgin ruwansu ya kife a tekun, kuma bayanan da aka samu daga wadanda suka tsira sun bayyana cewa akwai mutane sama da 200 a cikin jirgin ruwan.

Haka zalika an bayyana cewa, jirgin ruwan mallakar wani dan kasar Yaman da ke garin Ta'iz ne.

 


News Source:   ()