Ƴan cirani na cike da fargaba bayan nasarar Trump a zaɓen Amurka

Ƴan cirani na cike da fargaba bayan nasarar Trump a zaɓen Amurka

Alkaluma sun nuna cewa akwai ƴan cirani aƙalla miliyan 13 da zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda kuma Trump ya sha alwashin cewa daga kansu ne zai fara don mayar da su ƙasashensu.

Wasu bayanai sun ce tuni Trump ya fara tattara kundin ƴan ciranin don cika alƙawarinsa ta hanyar haɗa hannu da hukumomin kula da ƴan cirani da jami’an tsaro waɗanda da su ne za a gudanar da aikin.

Ko a wa’adinsa na farko Trump ya yi alƙawarin tisa keyar miliyoyin baƙi da ke zaune a Amurka amma kuma shirin nasa bai cika ba sakamakon tangarɗar da ya samu daga ɓangaren shari’a amma masana na ganin a wannan karon lamarin ya sha bamban.

Trump na da gagarumin rinyaje ta yadda jam’iyyarsa ke jagorancin majalisar dattijai wanda zai bashi damar samun sauƙin iya aiwatar da jerin manufofinsa da ke cin karo da ra’ayin Democrats.

Donald Trump ya alƙawarta cewa a wannan karon zan yi korar da ba a taɓa irinta ba a tarihin Amurka, ciki kuwa har da waɗanda suka samu izinin zama a baya-bayan nan.

Ƙarƙashin manufofin Trump kan ƴan cirani, shugaban na da nufin kwashe ƴan cirani aƙalla miliyan guda duk shekara, batun da masana ke gargaɗin cewa zai kai ga take haƙƙin ɗan adama baya ga raba tarin iyalai da juna.

Wata ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a a Amurkan ta nuna cewa kashi 39 na al’ummar ƙasar ne ke goyon bayan tisa ƙeyar ƴan ciranin zuwa gida yayinda kashi 56 ke son baiwa baƙin hauren takardun zama na dindindin a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)