Cikin rahoton da ta fitar IOM ta ce daga cikin baƙin da ke ganin takansu har da waɗanda ke kulle a gidajen da suke aiki babu damar fita, bayan tserewar da aka yi ba tare da su ba.
Shugaban ofishin hukumar ta IOM da ke Lebanon Mathieu Luciano, baƙi ‘yan ci rani daga ƙasashen Habasha da Kenya, da Sri Lanka, da Sudan, Bangladesh da kuma Phiippines kimanin dubu 170 ne akasarinsu mata ke aiki a Lebanon, da dama daga cikinsu kuma sun rasa tudun dafawa, abindaya sanya su fakewar wucin gadi a wuraren da suka rakuɓe, yayin da wasu kuma ke kulle a cikin gidajen da suke,, bayan da masu gidansu suka cika rigunansu da iska don gujewa hare-haren Isra’ila da ke hanƙoron murƙushe mayaƙan Hezbollah.
Babban jami’in na IOM ya ƙara da cewar babban ƙalubalen da suke fuskanta a yanzu haka shi ne rashin kuɗaɗen biyan buƙatun ɗimbin baƙin da ke neman agajin kwashe su zuwa ƙasashen su, waɗanda ya ce yawansu ƙaruwa yake a kullum.
Ya zuwa yanzu mutane fiye da dubu 2 Isra’ila ta kashe a Lebanon, tun bayan hare-haren da ta ƙaddamar daga rabar 23 na Satumban da ya gabata, a yankunan Kudanci da kuma sassan Beirut babban birnin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI