An bukaci kotu ta daure mutumin da yake hayar mutane su yiwa matarsa fyade

An bukaci kotu ta daure mutumin da yake hayar mutane su yiwa matarsa fyade

Wannan shari’a ta tada hankalin jama’ar kasar baki daya, ganin yadda Dominique Pelicot ya dinga hayar abokansa ta hanyar intanet suna yiwa matarsa Gisele Pelicot fyade, bayan ya dirka mata magungunan dake kawar da hankalinta.

Yadda mata ke zanga zanga a kan shari'ar Yadda mata ke zanga zanga a kan shari'ar REUTERS - Abdul Saboor

Laure Chabaud, daya daga cikin lauyoyin dake gabatar da karar, ta ce hukuncin kotun zai dada tabbatar da cewar fyade babban laifi ne a Faransa, kuma duk wanda aka samu da hannu a ciki ya zama wajibi a hukunta shi.

Chabaud ta ce hukuncin da alkalin kotun zai bayar zai taimaka gaya wajen zama izina ga wadanda ke aikata irin wannan laifin da kuma karfafa wadanda aka ci zarafin su cewar akwai hukunci a kan duk wanda ya taka doka.

Ma’aikatar shari’ar Faransa tace hukuncin da masu gabatar da karar suka nema, ya zarce adadin shekaru 11 da aka saba, yayin da masu gabatar da kara suka bayyana cewar wannan shari’ar ta sha banban da wadda aka saba gani, saboda haka ya dace a yi hukunci mai tsauri a wannan karon.

Shi Dominique Pelicot da ya dinga hayar mutane suna yiwa matar tasa fyade ya amsa laifinsa tare da neman afuwa, ya yin da ake karrama matar tasa Gisele a matsayin wata jarumar dake yaki da cin zarafin mata saboda yadda ta fito fili ba tare da boye kanta ba dan ganin na hukunta wadanda suka mata aika aikan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)