Gini na biyu mafi tsayi a duniya yanzu yana da otal a cikinsa.
Wani otal na kasaita ya buɗe ƙofofinsa ga baƙi a saman Hasumiyar Shanghai mai tsawon mita 632 da ke birnin Shanghai na China.
Otal din mai daki 165 yana ba da damar kallon birni daga wuri mafi tsayi.
Babban otal din na kasaita yana da abubuwan ban sha’awa da yawa.
Tunda otal ɗin yana da tsayin daruruwan mitoci, an tsara nau’rar kai mutane sama da kasan ginin na musamman. Na’urar zata iya kaiwa tsayin mita 18 a cikin dakika ɗaya.
Farashin dare na dakuna 34 a otal din suna cikin mafi tsada a duniya. Kudin kwana ɗaya a cikin irin ɗakunan ya kusan dala dubu 10 da 500.
Ma’aikatan otal din sun ce duk da tsadar da yake da, sha'awar zama a otal din na da yawa.