Kawo yanzu a fadin duniya Corona ta yi ajalin mutum dubu 371 inda kuma ta kama mutum miliyan 6 da dubu 161 haka kuma mutum miliyan 2 da dubu 738 sun warke.
An bude Masjid Al-AKsa domin fara yin ibadu bayan watanni biyu yana rufe sanadiyar kwayar cutar corona.
A sanadiyar annobar cikin awannin 24 da suka gabata an samu mutane 34 a Masar, 32 a Afirka ta Kudu, 8 a Algeria da Kamaru, 3 a Mali, 2 a Maroko da Djibouti, daya a Ghana, Senegal, Somalia, Kenya, Saliyo da Madagascar sun ra rasa rayukansu. Don haka, asarar rayuka gaba daya a cikin Nahiyar Afirka ya haura dubu 4 da 40. Adadin wadanada suka kamu da cutar a Nahiyar ya karu zuwa dubu 142 da dari 306, adadin wadanda suka murmure ya kai 60,000 da 153. A kasashen Eritrea, Lesotho, Namibia, Rwanda, Seychelles da Uganda, kawo yanzu ba a sami rahoton mace-macen mutane daga cutar ba.