An binne fararen hula 'yan kasar Azabaijan da Armeniya ta kashe ta harin bam a lokacin da suke kokarin binne mamaci a makabartar yankin Terter.
An yi wa mutanen jana'iza inda mata suka dinga kuka da kururuwa.
Makusantan wadanda suka mutun sun bayyana cewar suna yin jana'izar mamatansu da rana amma saboda tsoron kar a sake kai musu wani harin sai suka binne su da daddare.
A ranar Alhamis din nan ne Armeniya ta kai hari kan wata makabarta a yankin Terter na Azabaijan a lokacin da jama'a suka taru don binne wata gawar. An kashe mutane 4 tare da jikkata wasu 4 a harin.