Jami'an 'yan sanda 2 sun rasa rayukansu sakamakon hari da bindiga da aka kai musu a garin McAllen da ke jihar Texas din Amurka.
Daraktan 'yan sandan McAllen Victor Rodriguez ya shaida cewar an budewa 'yan sandan wuta a wani gida da suka kai farmaki.
Rodriguez ya ce 'yan sandan sun mutu nan take sakamakon bude musu wutar da aka yi.
Darakta Rodriquez ya kara da cewar maharin mai suna Aldon Caramillo ya kashe kansa bayan bindige 'yan sandan, kuma ya aikata manyan laifuka a baya inda ake zargin sa da mu'amala da miyagun kwayoyi da kai hare-hare.