An bindige 'yan sanda 2 a Afganistan

An bindige 'yan sanda 2 a Afganistan

'Yan sanda 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai a jihar Gazne da ke Afganistan.

Kakakin Fadar Gwamnan Gazne Wahidullah Jumazadah ya shaida cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka bude wuta kan jami'an 'yan sanda a tsakiyar jihar.

Jumazadah ya ce an kashe jami'ai 2 a harin, kuma maharan sun ranta a na kare bayan kai harin.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.


News Source:   ()