Ƴan bindiga sun buɗewa ƴan jarida wuta a yayin buɗe babban asibiti a Haiti

Ƴan bindiga sun buɗewa ƴan jarida wuta a yayin buɗe babban asibiti a Haiti

Hukumomi ba su bada alƙaluman waɗanda suka rasa rayukansu ba a harin na ranar Talata amma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ƴan jarida 2 da ɗan sanda 1 ne suka rasu kamar yadda wani ɗan jarida da ya ga yadda lamarin ya faru da bai yadda a ambaci sunanshi ba ya tabbatar.

Wannan ne hari na baya-bayannan da aka kai Haiti wadda ke fama da matsalolin tattalin arziƙi da na siyasa da ke karuwa tun bayan ƙashe shugaban kasar Jovenel Moise a shekarrar 2021.

Jami’an tsaro da hukumomin ƙasar na fama domin ganin bayan kungiyoyin masu aikata manyan laifuka, wanda ke ƙaruwa kuma ya kawo tsaiko a ƙasar. Wani abu da ake ganin ya tirsasa rufe asibitin mafi girma.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ƴan jarida sun taru da ƙarfe 11 agogon ƙasar wanda ya yi daidai da 16 agogon GMT amma kuma ƴan bindga suka buɗe wuta.

Hukumomi sun shirya buɗe asibitin a watan Uli amma harin bindiga da aka kai ya tirsasawa Firaministan ƙasar Garry Conille tserewa daga wurin bikin buɗewar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)