An baje kolin hotunan ranar 15 ga watan Yuli a NATO

An bude baje kolin hotuna a helkwatar kungiyar tsaro ta NATO da ke Brussels, babban birnin Beljiyom, a yayin bikin ranar 15 ga watan Yuli na Demokradiyya da Ranar Hadin Kan Kasar Turkiyya.

Wakilin din-din-din na Turkiyya a NATO Ambasada Basat Ozturk, Mataimakin Sakatare Janar na NATO Baiba Braze, wakilan dindindin na wasu kasashen NATO, jami’ai daga rundunar sojan Turkiyya da wakilan diflomasiyya da jami’an NATO sun halarci bude baje kolin.

Ambasada Ozturk, a jawabinsa a wurin bude taron wanda wakilcin Turkiyya na din-din-din ya shirya a NATO, ya ce sun shirya irin wannan baje kolin ne domin tunawa da yunkurin juyin mulkin da Kungiyar ta'adda ta Fetullah (FETO) ta yi a ranar 15 ga watan Yulin 2016.

Ozturk ya bayyana cewa, Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg na daya daga cikin shugabannin farko da suka la’anci yunkurin juyin mulkin tare da nuna hadin kai ga Turkiyya, kuma Sakatare Janar din ya ziyarci Majalisar Dokokin Turkiyya (TBMM), dake Ankara babban birnin kasar inda aka tayar da bam a daren yunkurin juyin mulkin.


News Source:   ()