An baiwa yarinyar da ta dauki bidiyon kashe George Floyd lambar yabon Pulitzer

An baiwa yarinyar da ta dauki bidiyon kashe George Floyd lambar yabon Pulitzer

Darnella Fraizer, wacce ta dauki bidiyon mutuwar George Floyd yayin da ‘yan sanda ke kokarin kamashi a jihar Minnesota a Amurka, an ba ta Kyautar Pulitzer.

Kwamitin Kyautar Pulitzer ta sanar da cewa bidiyon da aka dauka dake nuna mutuwar Floyd a hannun 'yan sanda a jihar Minnesota ya ja hankalin al'umman Amurka da ma duniya baki daya. Hakan ya sanya bayar da kyuata ta musamnan ga wacce ta dauki bidiyon.


A cikin sanarwar, an jaddada cewa Fraizer, wacce ta yi rikodin lokacin da jami'in dan sanda Derek Chauvin ya danna gwiwarsa a wuyan George Floyd, kuma ya yi sanadin mutuwarsa, tana da shekaru 17 a lokacin ta bayar da gudunmowa ga mahimmiyar rawar da ‘yan jarida ke takawa a kasa wajen neman adalci.

Bidiyon Fraizer, wanda ya nadi labarin abin da ta gani lokacin da take wucewa ta hanyar kwatsam ya taimakawa 'yan jaridu. Ta bayyana cewa rahoton da dan sanda Chauvin ya bayar game da lamarin ba gaskiya ba ne, kuma an kira yarinyar domin ta bayar da shaida a zaman jin yadda Floyd ya mutu.

Kyaututtukan Pulitzer ana bayar dasu ne ga wadanda suka yi muhimmin aiki a fannin aikin jarida. Kyautace ta girmamawa wanda Joseph Pulitzer ya kafa a shekarar 1917.

A garin Minneapolis, Ba’amurke dan asalin Afirka, mai shekara 46, George Floyd ya yi roko na mintuna “Ba zan iya numfasawa ba” lokacin da jami’in dan sanda mai shekaru 44, Derek Chauvin ya danna gwiwa a wuyansa tsawon minti 9 da dakika 29 ya yin kamashi bisa zargin yaudara a ranar 25 ga Mayu, 2020, kuma ya mutu bayan wani lokaci.


News Source:   ()