An baiwa mata 'yan sanda damar daura dankwali a jihar New Jersey dake Amurka

Mata 'yan sanda za su iya yin aiki tare da dankwali da lullubi a a birnin Newark dake jihar New Jersey a Amurka.

Brian O'Hara, Daraktan Tsaron Jama'a na Newark, ya bayyana a taron manema labarai cewa suna daraja imani,

"Wannan shawarar za ta taimaka mana wajen tabbatar da cewa muna mutunta imanin mutane."

A wurin taron, magajin garin Newark Ras Baraka ya tunatar da cewa Sashin ‘yan sanda na Newark shi ne wuri na farko a kasar da za su ba wa Musulmai da Sikh damar ajiye gemu daidai da imaninsu.

An lura cewa bukatar da wata 'yar sanda mace musulma ta gabatar na da tasiri a shawarar da aka ba ta na yin aiki da alkyabba a cikin gari.


News Source:   ()