An baiwa kare gadon dala miliyan 5 a Amurka

An baiwa kare gadon dala miliyan 5 a Amurka

A jihar Tennessee dake kasar Amurka wani kare ya gaji dala miliyan 5 kimanin naira miliyan dubu 2,500 daga mamacin mamallakinsa.

An bayyana cewa wani dan kasuwa mai suna Bill Doris da ya mutu karshen shekarar 2020 ya bar wasiyar baiwa karensa jinsin Birder Collie dan shekara 8 mai suna Lulu gadon dalar Amurka miliyan biyar.

Doris, a wasiyar da ya rubuta ya bayyana cewa ya baiwa karen gadon ne domin a rinka biyar wacce za ta rinka kula da karen wato Martha Burton kudaden kula dashi ko wane wata.

Mai kula da Lulu ta ce ba ta san ko za ta iya kashe dala miliyan 5 a kan kare ba, amma tana son gwadawa.

An bayyana cewa dai mamacin mamallakin karen dan kasuwa ne wanda bai da aure.

 


News Source:   ()