Ƴan ƙasar Venezuela sun ci gaba da zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓe

Ƴan ƙasar Venezuela sun ci gaba da zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓe

Zanga-zangar da aka yi a farkon makon nan ta koma tarzoma wanda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 11 yayin da aka kama daruruwa.

Masu zanga-zanga a titunan babban birnin kasar sun ɗaga tutoci tare da rera taken kasar domin nuna goyon bayansu ga dan takarar 'yan adawa da suke ganin shi ya lashe zaben shugaban kasa da gagarumin rinjaye.

Hukumomi sun ayyana shugaba Nicolás Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Lahadin da ta gabata amma har yanzu ba su fitar da adadin kuri’un da za su tabbatar da cewa ya yi nasara ba.

Shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro. Shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro. © Fernando Vergara / АР

A maimakon haka, gwamnati ta kama daruruwan magoya bayan ‘yan adawa wadanda suka fito kan tituna kwanaki bayan zaben da aka yi ta cece-kuce, kuma shugaban kasar da ‘yan majalisarsa sun yi barazanar ɗaure shugabar ‘yan adawa, María Corina Machado, da dan takararta na shugaban kasa Edmundo Gonzalez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)