An ajiye bam a akwatin gidan wayan kungiyar Turkawa a Switzerland

An ajiye bam a akwatin gidan wayan kungiyar Turkawa a Switzerland

An ga wani bam da ke shirin fashewa a cikin akwatin gidan waya na hedikwatar Kungiyar Turkawa ta Switzerland (ITT), jagorar kungiyoyi masu zaman kansu na Turkawa dake yankin Rumlang a kasar Switzerland.

Shugaban ITT Seref Yıldız, wanda magoya bayan kungiyar ta'adda aware ta PKK suka sha kaiwa hare-hare har da ya tilsatu da ya yin kaura daga gidansa ya bayyana cewa,

"An sanya bam a cikin akwatin gidan waya na ITT tsakanin 13.30 zuwa 14.00 a jiya. Na lura da lamarin ganin murfin akwatin a bude yake. Nan take na kira 'yan sanda," 

'Yan sanda na ci gaba da bincike akan lamarin.

Magoya bayan PKK sun kai hari kan kamfanoni da kungiyoyin Turkiyya a Switzerland a watannin baya-bayan nan.


News Source:   ()