Wani mutum ko wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun aika wasikar cin mutuncin Musulmi da Musulunci zuwa Masallacin Yeni Beyazıt da ke Hamburg a kasar Jamus.
Wasikar wacce ta yi cin zarafi da batanci ga addinin Islama, wacce kuma ke dauke da zagi na kunshe da kalamai da hotunan nuna kiyayya ga Musulmai.
A sakon da aka sanya a shafin sada zumunta na masallacin, an la'anci mutum ko mutanen da suka aiko da wasikar. Inda aka tabbatar musu da cewa,
"Wannan ba kasarku ba ce, kasarmu ce. Muna zaune a nan kuma anan zamu ci gaba da zama, ya kamata ku san da haka"