A jihar New Jersey dake kasar Amurka an gudanar da zanga-zangar kalubalantar yunkurin Isra'ila na mamaye yankin Zirrin Gaza.
Kungiyoyin mabiya darikar Ortodoks Yahudawa da Musulmi sun gudanar da zanga-zangar kalubalantar yunkurin mamaye yankin Falasdin da Isra'ila ke yi.
Masu zanga-zangar na dauke da allunan da aka rubuta "Rayuwar Falasdinawa nada daraja", "Neman 'yancin Yahudawa" domin kalubalantar yunkurin mamaye Zirrin Gaza.
Daga cikin masu zanga-zangar sun hada har da yara. dauke da tutocin Falasdin.