Dubunnan mutanen da suka taru a Washington, babban birnin Amurka a jiya, sun yi tattaki daga Tumbin Washington zuwa ginin Majalisar domin tallafawa Falasdinu da mayar da martani ga Isra'ila.
Da suka taru a gaban Husaimmiyar Washington da ke tsakiyar gari tare da rike tutocin Falasdinu a hannunsu, mahalarta taron sun rera taken "'Yanci ga Falasdinu".
Masu zanga-zangar, wadanda suka mayar da martani ga gwamnatin Amurka, wacce ta yi shiru game da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Falasdinawa, sun ci gaba da maci, tun daga Tumbin Washington, zuwa gaban ginin Majalisar Dokokin Amurka.
Tattakin nuna goyon baya ga Falasdinu, wanda ya dauki kimanin awanni 3, ya kare ba tare da wata matsala ba.