Yayin da ya ke jawabi gaban ɗumbin magoya bayan jam'iyyar Demokrat a babban taronsu da ke gudana a Chicago, Obama wanda ya jinjina tare da bayyana goyon bayansa takarar Khamala Haris, ya ce itama a shirye take ta ƙarbi ragamar jagorancin ƙasar Amurka.
Muna da damar zaɓar wadda ta yi amfani da rayuwarta kachokan wajen ba wa mutane dama kamar yadda Amurka ta ba ta.
Trump na da haɗari
Tsohon shugaba Obama, wanda ya samu kyakyawar tarba da tafi da murna a filin da ya cika makil, ya ce mataimakiyar shugaban ƙasa Harris za ta yi wa Amurkawa yaki, inda ya kira abokin takararta na zaɓen watan Nuwamba Donald Trump a matsayin mai tattare da haɗari.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren ƙadan daga cikin fassarar kalaman Barack Obama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI