Amurkawa na shagulgulan murnar dawowar Donald Trump kan kujerar mulkin ƙasar

Amurkawa na shagulgulan murnar dawowar Donald Trump kan kujerar mulkin ƙasar

Tun a yammacin jiya aka fara bukukuwan rantsar da zababben shugaban Trump wanda ya kunshi gangamin dubban magoya bayansa da kuma aje firanni a inda ake gudanar da bikin tuna sojojin da suka bada gudumawa wajen kare Amurka.

Cikin bukukuwan da aka gudanar kafin rantsuwar da shugaban zai karba a yau Litinin, sun hada da taron gangamin sake gina Amurka da wasannin kwallon gora da na kwando, duk da soke wasu bukukuwan saboda tsananin sanyin da ake yi a Washington.

Akasarin magoya bayan Trump sanye da jajayen riguna da kuma hula sun yi jerin gwano a Washington inda suke daga muryoyinsu suna rera USA, USA.

Tuni dai aka girke jami'an tsaro daban daban a kewayen fadar shugaban kasa da kuma majalisar dokoki domin kare lafiyar mutanen da za su halarci bikin rantsar da shugaban.

Ana saran sabon shugaban ay fara aiki nan take bayan karbar rantsuwa da daukar matakai a bangaren bakin dake zuwa Amurka da shirin samar da makamashi kamar yadda mai bashi shawara a kan harkokin tsaro Mike Waltz ya bayyana.

Masu shirya bikin ranstuwar sun ce takaitattun mutane ne za su halarci bikin rantsuwar da aka mayar cikin majalisar dokoki saboda tsananin sanyi, kuma akalla jami'an tsaro dubu 25 za su yi aiki a wurin da kewayensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)