Amurkawa na dakon ganin wanda Harris za ta zaɓa mataimakinta

Amurkawa na dakon ganin wanda Harris za ta zaɓa mataimakinta

Ya zuwa wannan lokaci dai babu wanda ke da tabbas kan wanda Kamala Harris za ta zaɓa a matsayin mataimakinta.

Sai dai akwai wasu fitattun mutane kimanin 10 da  wasu majiyoyi ƙwarara suka ambata cewar mai yiwuwa Harris ta zaɓi Andy Beshear gwamnan jihar Kentucky wanda ke shan yabo saboda muhimman ayyukan ci gaba da yake aiwatarwa tun daga shekarar 2019 zuwa yanzu.

Sauran mutanen da ake tunanin Kamala Harris ka iya zaɓar mataimaki daga cikinsu sun haɗa da Sakataren Kula da Harkokin Sufuri Pete Buttigieg, wanda a shekarar 2020 ya yi takara da Biden da kuma Harris ɗin yayin zaɓen fidda gwanin jam’iyyar Democrats.

Akwai kuma Roy Cooper gwamnan North Carolina da kuma Mark Kelly, Sanata mai ci daga Arizona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)