Amurkawa miliyan 240 za su zaɓi sabon shugabansu a ranar Talata

Amurkawa miliyan 240 za su zaɓi sabon shugabansu a ranar Talata

Duk da yawan adadin masu kaɗa kuri’ar, hankula sun fi karkata ne kan wasu tsirarun jihohi da ake kira Swing State waɗanda ke fayyace wanda zai ɗare kan karagar mulki.

Waɗannan jihohin a bana sun haɗa da Arizona da Georgia da Michigan da Nevada da North Carolina da Pennsylvania da kuma Wisconsin.

Ba abin mamaki ba ne yadda ƴan takarar manyan  jam’iyyun Democrat da Republican ke dagewa kwarai wajen yaƙin neman zaɓe a waɗannan jihohi masu matuƙar tasiri da wahala.

Jam’iyyun Democrat da Republican na kusan kan-kan-kan ne a waɗannan jihohin. Ma’ana babu wacce za a iya cewa za ta samu nasara kai-tsaye har sai an kammala fafatawa.

Sai kuma jihohin da ake kiran su safe states, abin da ke nufin cewa, jam’iyya guda na da kwarin guiwar cewa, ita ce za ta fi samun yawan ƙuri’u da tazara mai yawa.

Yanzu bari mu yi maganar tsarin nan na Electoral College, inda kowacce jiha a Amurka ke zaɓen wakilan da su ne daga bisani ke fayyace ainihin wanda zai zama shugaban ƙasa.

Kowacce jiha a Amurka , na da adadin wakilan Electroral College daidai da yawan wakilanta a majalisar dattawa da ta wakilai.

Misali, jihar Carlifornia, na da wakilan Electoral College guda 54, abin da ya yi daidai da adadin wakilanta a majalisar dattawa mutum biyu da kuma wakilanta a majalisar wakilai mtuum 52.

Ɗan takara na buƙatar samun wakilai 270 daga cikin jumullar wakilai 538 kafin samun nasarar shiga fadar White House.

Ƙarin bayani a nan shi ne, Amurkawa masu kaɗa kuri’a, ba wai suna zaɓen shugaban  ƙasa ba ne kai tsaye, a’a, suna zaɓen wadannan wakilan ne da ke zaɓen shugaban ƙasa daga bisani.

Don haka, abu ne mai yiwuwa ɗan takarar da ya fi samun yawan kuri’un jama’a a zaɓen Amurka ya gaza samun nasarar shugaban ƙasa muddin bai samu adadin da ake buƙata ba na waɗannan wakilai da ake kira Electoral College.

Wannan ke ɗaɗa nuna muhimmancin waɗancan jihohi da suka fi yawan wakilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)