Amurkawa 'yan asalin Afirka sun gargadi Biden

Amurkawa 'yan asalin Afirka  sun gargadi Biden

Amurkawa'yan asalin nahiyar Afirka sun gargadi dan takarar Shugaban Kasar na jam'iyyar Democrats Joe Biden da cewar matukar bai yi alkawarin kawo sauyi a aiyukan 'yan sandan Amurka ba, to zai iya rasa goyon bayansu.

A lokacinda aka fara muhawara kan yin kwaskwarima ga aiyukan 'yan sandan Amurka tun bayan kashe bakar fata George Floyd a ranar 25 ga watan Mayu, idanuwa sun koma kan Shugaban Amurka Donald Trump da abokin hamayyarsa a zaben da za a yi a 2020, dan jam'iyyar Democrats Joe Biden.

A wata wasika da kungiyoyi sama da 50 da aka kafa don kare martabar 'yan asalin Afirka a Amurka suka aikawa Biden, sun ce alkwarin ware dala miliyan 300 don yin kwaskwarima ga 'yan sandan Tarayya, ba zai warware matsalolin da ake fuskanta ba a kasar.

A wasikar an bayyana cewar "Komawa daidai ba zai warware abubuwa ba. A wajen 'yan asalin Afirka, komawa daidai shi ne zalunci, tsoro da nuna wariya gare su."

Wasikar ta yi kira ga Biden da ya dauki karin matakai game da batun na yi wa aiyukan 'yan sanda kwaskwarima a Amurka, idan kuma ba haka ba to zai iya rasa goyon bayan 'yan asalin Amurka a zaben Shugaban Kasar da za a gudanar a watan Nuwamba.


News Source:   www.trt.net.tr