Amurkaa ta gargaɗi jama'a kan guguwar ibtila'in guguwar Milton

Amurkaa ta gargaɗi jama'a kan guguwar ibtila'in guguwar Milton

Hukumomi a Amurka sun ce a wannan Talata guguwar Milton mai lamba 4 za ta kara girma, yayin da ta yi barazana ga tsibirin Yucatan na ƙasar Mexico a kan hanyarta ta zuwa Florida, inda aka umarci sama da mutane miliyan guda da su kaurace wa hanyarta.

Gabar yammacin Florida mai yawan jama’a, wanda har yanzu bata gama murmurewa daga mummunar guguwar Helene da ta afkawa mata makwanni biyu da suka gabata, na fuskantar karin wata barazana a ranar Laraba.

Cibiyar kula da guguwa ta Amurka ta yi hasashen cewa, Milton na iya afkawa babban birnin Tampa Bay, mai dauke da mutane sama da miliyan 3.

Cibiyar ta ce, Milton za ta ci gaba da zama guguwa mai matukar haɗari da Florida zai fuskanta, wanda tace zata yi mummunar barna, tare da katse wutar lantarki na kwanaki a yankin.

Ya zuwa ƙarfe 10 na safiyar Talatan nan  agogon ƙasar, guguwar na kilimita 105 daga arewa maso gabashin babban birnin jihar Yucatan na ƙasar Mexico, kan hanyarta zuwa Florida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)