Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka, Manjo Janar Pat Ryder ya bayyana cewar sakataren tsaron ƙasar Lloyd Austin ya bada umarnin tura sojojin, da kuma na'urar kakkabo makaman Israila domin taimaka mata.
Janar Ryder ya ce makaman za su taimakawa Israilar kare kanta daga duk wani irin makamin da za a harba mata daga ƙasashen ƙetare, ganin yadda ƙasar Iran da ƙungiyar Hezbollah ke mata ruwan makamai masu linzami.
Jami'in ya ce wannan wani tabbaci ne na matsayin Amurka dangane da kare Isra'ilar da kuma Amurkawan da ke zaune a cikin ta.
Wannan makami na THAAD da za a kai wa Israila wani ci gaba na makamin Patriot wanda ke iya kakkabo duk wani makami mai linzami da aka harba a sararin samaniyar ƙasar, da kuma kai hari mai nisan kilomita tsakanin 150 zuwa 200.
Ya zuwa yanzu dai ba a iya tantance ko daga ina za a kai makamin ba, sai dai rahotanni sun nuna cewar a shekarar da ta gabata, Amurkar ta aike da irin wannan makami yankin Gabas ta Tsakiya domin kare sojojin ta da ke yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI