Mijin mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris, Doug Emhoff, a ranar Alhamis da ta gabata ya sanarwar da cewa Amurka za ta ba da gudummawa ta musamman sama da dala miliyan biyu ga hukumar raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO don bunkasa yaki da kyamar Yahudawa.
Bayanan Emhoff, tsohon babban lauyan nishadantarwa a kasar, ya samu cigaba a 'yan makonnin nan bayan da Harris ta zama ƴar takarar jam'iyyar Democrat a zaben shugaban Amurka da da zata kara da Donald Trump na Republican a daidai lokacin da shugaba Joe Biden ya janye daga takararsa.
Wannan ya ɗaga tsammanin zai iya zama ɗan Adam na farko a Amurka idan Harris ta zama mace ta farko da ta zama shugabar Amurka bayan zaɓen dake tafe a watan Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI