Amurka za ta ƙara yawan dakarunta a Gabas ta tsakiya - Pentagon

Amurka za ta ƙara yawan dakarunta a Gabas ta tsakiya - Pentagon

Kakakin Pentagon Sabrina Singh ta ce Amurkan za ta ƙara yawan dakarun na ta zuwa dubu 43 a yankin gabas ta tsakiya, wanda zai ƙunshi ƙara yawan hatta kayakin yaƙinta da suka haɗa da jiragen Soji da na kai farmaki.

Tun bayan tsanantar rikicin Isra’ila da Hezbollah wanda ya kai ga kisan jagoran ƙungiyar Sayyed Hassan Nasrallah, fargaba ta baibaye yiwuwar ta’azzarar yaƙin zuwa wasu sassa na gabas ta tsakiya.

A cewar Pentagon da ma ta yi zama cikin shiri saboda abin da ka je ya zo, wanda ke nuna cewa dole ta girke ƙarin dakaru don baiwa Isra’ila kariya.

Pentagon ta bayyana cewa cikin sabuwar rundunar da za ta aike gabas ta tsakiya za ta ƙunshi tarin jiragen yaƙi da suka haɗa da nau’ikan F-15E da na kai farmaki kirar F-16, da kuma na yaƙi ƙirar F-22 kana A-10.

Ma’aikatar ta Pentagon ta ce wannan sabuwar runduna za ta isa gabas ta tsakiya ne don ƙara ƙarfi kan dakarun da tun tuni suke a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)