Amurka ta zargi Rasha da yunkurin yin katsalandan a zaben watan gobe

Amurka ta zargi Rasha da yunkurin yin katsalandan a zaben watan gobe

Fadar White house ta ce ana zargin Rasha ta fara tura ƴan leƙen asiri zuwa cikin ƙasar waɗanda aka ɗora musu alhakin yiwa shafin fadar shugaban ƙasa kutse, da kuma shirya hare-haren ta’adanci.

Tuni dai aka kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi tare da fara tuhumarsu da laifin yunƙurin shirya ta’addanci a lokacin zaɓen tare da ƙwace wasu shafukan internet mallakin Rasha guda 32 da hukunta wasu ƴan ƙasar guda 10.

Antoni janar na Amurka Merrick Garland ya ce an ɗauki wannan mataki ne la’akari da yadda bayanan sirri suka fara nuna yadda Rasha ke amfani da wasu ƴan ƙasar ta da kuma Amurkawa wajen yaɗa farfaganda da kuma labaran ƙarya a game da zaɓen.

Cikin manyan hukumomin Rasha da Amurka ta hukunta kawo yanzu har da babbar kafar yaɗa labaran ƙasar RT.

Amurka ta ce ta kuma gano yadda Rasha ta kammala duk wani shirri na watsa labaran ƙarya da yamutsa zaben watan Nuwamba mai zuwa.

Misalin irin wannan aniya da Rasha ta dauka har da yaɗa labaran ƙarya kan baƙin haure aikata laifuka, samar da ayyukan yi da kuma yaƙin Gaza a cewar Amurkan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)