Kasar Amurka ta fito karara ta zargi Moscow da laifin kara gurbata rikicin kasar Libiya inda ta yi kira da a bi hanyar diflomasiyya domin kawo karshen rikicin kasar.
Hakan ya biyu bayan rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar wanda ya tabbatar da cewa mayaka masu zaman kansu daga Rasha su na yaki a madadin Janar Khalifa Haftar a kasar ta Libiya.
Rahoton da aka kaiwa kwamitin tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a makon jiya wanda jami'an diflomasiya suka bayyana wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa ta (AFP) ya nuna cewa akwai kimanin mayaka daga Rasha masu zaman knasu 800 zuwa 1,200 daga kanfanin Wagner Group na Rasha dake goyon bayan Janar Haftar a Tripoli.
Jaridar Daily Sabah ta rawaito cewa mayakan sun kwashe kusan shekara guda kenen su na gwabza yake-yake domin goyawa Janar Haftar baya a kasar ta Libiya.
Wani jami'in ma'aiktar harkokin wajen Amurka Chris Robinson ya bayyna cewa goyawa Janar Haftar baya da Rasha ke yi ya kara tabarbare zaman lafiyar kasar inda ya kara jefa al'uman kasar cikin halin kaka-nikayi.