Amurka ta zabtare kashi 90% na tallafin da take bai wa ƙasashe

Amurka ta zabtare kashi 90% na tallafin da take bai wa ƙasashe

Tun a ranar farko da ya kama aiki a matsayin shugaban ƙasa, Trump  ya rattaba hannu kan wata doka da ke soke ɗaukacin tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashe daban-daban na duniya, yana mai cewa, gwamnatinsa za ta sake nazari game da yadda ake kashe waɗannan kudaɗe.

Gwamnatin ta bayyana aniyarta ta yin fatali da duk wani shiri da ya yi hannun riga da manufofin Trump na sanya “ Amurka a Sahun Gaba”.

Sai dai a Talatar da ta gabata, wani alkalin kotun tarayya ya bai wa gwamnatin Trump wa’adin ƙasa da makwanni biyu da ta saki kuɗaɗen tallafin da ta dakatar.

Kodayake gwamnatin ta Trump ta garzaya Kotun Koli domin kalubalantar hukuncin kotun tarayyar, inda kuma ta yi nasara.

Yanzu dai gwamnatin Trump ta dage kan cewa, soke wancan tallafin, zai ba ta damar gudanar da wasu ayyukan jin-ƙai da ta ce za a fi ganin tasirinsu, sannan kuma sun yi daidai da manufofin Trump na sanya “Amurka a Sahun Gaba”.

Gabanin dakatar da ayyakanta, hukumar USAID na gudanar da ayyukan jin-ƙai a sassan duniya, inda take bada agajin gaggawa a ɓangaren kiwon lafiya a ƙasashe 120.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)