Amurka ta yi kira ga 'yan kasarta dake Afghanistan da su gaggauta ficewa daga kasar

Amurka ta yi kira ga 'yan kasarta dake Afghanistan da su gaggauta ficewa daga kasar

Ofishin jakadancin Amurka a Kabul ya yi kira ga 'yan kasarta da ke Afganistan da su gaggauta ficewa daga kasar saboda hadarin tsaro.

A cikin gargadin da aka yada a shafin yanar gizon ofishin jakadancin Amurka da ke Kabul, an nemi 'yan Amurka da su fice daga Afghanistan cikin gaggawa ta amfani da jiragen kasuwanci masu dacewa.

An ba da rahoton cewa mutanen da ba za su iya siyan tikiti na iya tuntubar Ofishin Jakadancin don taimako.

Sanarwar ta kuma nuna cewa karfin Ofishin Jakadancin na taimakawa 'yan kasa yana da iyaka saboda yanayin tsaro da karancin ma'aikata.


News Source:   ()