A lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai game da wancan zargin harin da ake ganin Isra’ila za ta iya kaiwa, Biden ya ce za su tattauna matakin da ya kamata ace sun dauka, kan hare-haren makamai masu linzami da Iran ta harbawa Isra’ila.
Ya ce tuni ya tuntuɓi shugabannin ƙasashen da ke ƙarkashin ƙungiyar G7 kan lamarin, kuma sun ce Isra’ila na da damar mai da martani.
Kawo yanzu dai, fadar White House ba ta bayyana matsayinta na irin martanin da ta ke son Isra’ila ta maida wa Iran ba.
Ana dai zaman ɗar-dar ne tsakanin Iran da Isra’ila, tun bayan harin ranar Talata ta Iran kai, wanda ta ce martani ne game da yadda Isra’ilan ke kai hare-hare cikin Lebanon da kuma kisan shugabannin ƙungiyoyin Hamas da Hezbolla da ta yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI