Amurka ta sanya masu safarar miyagun ƙwayoyin cikin kungiyoyin ta'addanci

Amurka ta sanya masu safarar miyagun ƙwayoyin cikin kungiyoyin ta'addanci

Sanarwar da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fitar, ta ce ƙungiyoyin na da haɗari ga tsaron Amurka da manufofin ketare da kuma muradun tattalin arziki.

Trump, ya bukaci hukumomin da abun ya shafa da su ayyana gungun masu aikata laifuka ko kuma manyan ƙungiyoyin da ke safarar miyagun ƙwayoyi a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci.

A farkon wannan watan ne Trump ya jinkirta wani mataki na sanya haraji mai tsauri kan Mexico da Canada, saboda abin da ya ce rashin hadin kai wajen dakile matsalar baƙin haure da safarar miyagun ƙwayoyi.

A farkon makon nan ne hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA, ta aike da wasu jirage marasa matuƙa zuwa Mexico, domin gudanar da bincike.

Shugaban Mexico Claudia ya ce shawagin jiragen wani bangare ne na hadin gwiwa da Amurka, waɗanda ke aikin sintiri bisa sahalewar doka.

A lokacin wa’adinsa na farko, Trump ya so yanke shawarar ayyana wasu 'yan kasuwa a matsayin 'yan ta'adda, amma a ƙarshe ya kawar da matakin.

Wasu manyan jami’an Amurka a lokacin sun bayyana rashin jin daɗinsu, yayin da suke ganin matakin na iya lalata dangantaka tsakanin ƙasar da Mexico, da kuma kawo cikas ga shirin yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Wani abin damuwar da ake gani shi ne, hakan zai iya sauƙaƙawa baƙin hauren samun mafakar shiga Amurka, ta hanyar amafani da sunan tserewa ayyukan ta'addanci.

Bayan hawansa mulki, Trump ya kuma umurci gwamnatinsa da ta shirya yiyuwar amfani da dokar yaƙi da aka samar a 1798, wadda za ta iya ba shi damar korar wasu da ake zargin 'yan kungiyar safarar miyagun kwayoyi ne ba tare da sauraron umarnin kotu ba, ko da yake har yanzu bai ɗauki wannan matakin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)