Wannan sabon tallafin da aka sanar kwanaki kadan gabanin zaben shugaban kasar Amurka, ya hada da na'urorin kariya na jiragen sama, da harsasai, da motoci masu sulke, da kuma na tankokin yaki, kamar yadda ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar a cikin wata sanarwa.
Za a fitar da wadanan kudade kai tsaye daga asusun kasar Amurka.
Washington "za ta ci gaba da aiki don amsa bukatun gaggawa na Ukraine a fagen fama don kare kanta daga Rasha.
A jiya Amurka ta bayyana cewa dakaru 8,000 na Korea ta Arewa na kan iyaka da Ukraine.
Goyon bayan Amurka ga yakin Ukraine © APDa yake ambato ma'aikatan leken asirin Amurka, shugaban diflomasiyya Antony Blinken ya nuna cewa daga cikin sojojin Korea ta Arewa 10,000 da a cewar Washington, suka shiga Rasha, har 8,000 "an jibge su a yankin Kursk", a Rasha, a kan iyaka da Ukraine.
A baya-bayan nan dai Korea ta Arewa ta kara karfafa alakar soji da birnin Moscow, inda a watan Yuni shugaban kasar Rasha ya kai ziyara a Pyongyang, inda ya kulla yarjejeniyar tsaro da Kim Jong Un.
Shugaban Ukraine da wasu Shugabanin kasashe masu dafawa Ukraine a yakin da ta ke yi da Rasha AP - Christinne MuschiAmurka ita ce babbar mai goyon bayan soji ta kyiv, tare da taimakon sama da dala biliyan 60 na taimakon soji tun lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine a watan Fabrairun 2022.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI