Amurka ta sake lafta takunkumai kan Iran game da harinta a Isra'ila

Amurka ta sake lafta takunkumai kan Iran game da harinta a Isra'ila

Dai dai lokacin da mahukuntan Isra’ila ke ci gaba da jaddada shirin ɗaukar fansar harin kan Iran musamman ta hanyar kai farmaki sashen makamashin ƙasar, Amurka ta yi gaban kanta wajen lafta takunkuman kan Tehran wadda ta jima ta na fama da tarin takunkumai.

Sai dai wannan sabbin takunkumai na Amurka za a iya cewa baza su yi tasiri kamar yadda ƙasar ke hasashe ba, lura da cewa dama sashen makamashin na Iran na fama da manyan takunkuman ƙasashen yammaci.

Babu tabbacin takunkumin na Amurka ya hana Iran ko kamfonin da ke aiki da ita dama jiragen dakon mai ci gaba da hada-hadar da ƙasar ta gabas ta tsakiya, lura da cewa dama takunkuman da ke kanta sun hanata iya hada-hada a bayyane face ta ɓarauniyar hanya.

A ranar 1 ga watan da muke ciki na Oktoba ne Iran ta kai hare-hare da makamai masu linzami kan Isra’ila don fansar kisan jagoran Hamas Isma’il Haniyeh da kuma jagoran Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah da Isra’ilan ta kashe a hare-haren da ta kai kansu a birnin Beirut na Lebanon.

Harin na Iran ya sanya fargabar rincaɓewar rikici a gabas ta tsakiya musamman bayan da Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani.

Amurka ta ce sabbin takunkuman za su shafi kamfanoni 6 da jiragen dakon mai 17 cikinsu har da na ƙasashen Hadaddiyar daular Larabawa da China da Panama da sauran wasu ƙasashe waɗanda za a haramta musu kasuwanci da Amurkawa baya ga kullewa da kuma ƙwace dukkanin dukiyoyinsu da ke cikin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)