Amurka ta raina dokokin duniya saboda tarbar Netanyahu - Amnesty

Amurka ta raina dokokin duniya saboda tarbar Netanyahu - Amnesty

A shekarar 2024 ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bayar da sammacin kamo mata Netanyahu da kuma tsohon ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant, sakamakon samunsu da aikata laifukan yaki akan al'ummar Falasdinu.

A ranar Talata majalisar dattijan Amurka ta yi watsi da wani kudiri  da ya nemi a sanyawa ICC takunkumi, bayan sammacin da ta fitar.

Dama kwararrun Majalisar Dinkin Duniya hadi da wasu manyan jami'an kotun ta ICC, sun nuna adawa da kudirin, tare da gargadin ba komai hakan zai haifar illa rashin tabbas ga dokokin kasa da kasa.

Da dama daga cikin masu goyon bayan kudirin na zargin ICC da nuna son kai wajen yanke hukuncin, zargin da kotun ke ci gaba da musantawa.

Wannan karon farko da Benjamin Netanyahu, ya kai ziyara wata kasa, tun bayan hukuncin kotun ta ICC a watan Nuwamban bara.

Isra'ila dai ta yi wasti da zarge-zargen da ake mata, tana mai cewa ba zzata rusunawa matsin lambar da ake mata ba, yayin da take kokarin kare 'yan kasarta.

Amurka wadda ba mamba bace a kotun ta duniya, itama ta yi watsi da zarge-zargen da ake yiwa Netanyahu da Gallant.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)