Amurka ta kori yara kanana masu neman mafaka akalla dubu daya

Amurka ta kori yara kanana masu neman mafaka akalla dubu daya

Duk da matsalar annobar Corona (Covid-19) da ake ciki, daga watan Maris zuwa yau Amurka ta kori yara kanana masu neman mafaka akalla dubu daya.

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya(UNICEF) ya bayyana cewar Amurka ta kori akalla yara kanana akalla dubu daya da ba su da masu kula da su zuwa kasashen Mekziko, El-Salvador, Guatemala da Honduras.

Sanarwar ta ce a dai wannan lokaci kasar Mekziko ma ta kori yara kanana masu neman mafaka 447 zuwa kasashen Guatemala da Honduras.

UNICEF ta yi gargadin cewar akwai yiwuwar yaran kanana su fuskanci nuna wariya a kasashensu bisa zargin sun kamu da cutar Corona.


News Source:   www.trt.net.tr