
Asusun Pepfar da ke kula da ayyukan bayar da agajin yaƙi da cutar HIV ƙarƙashin ofishin shugaban Amurka a Afirka ta kudu, wanda kuɗaɗen tafiyar da shi ke fitowa daga hukumar USAID ya wayi gari da jin wannan dakatarwar da ta shafi dukkanin kuɗaɗen da ya ke samu.
Dakatar da wannan agaji a cewar Desmond Tutu, shugaban gidauniyar yaƙi da HIV a Afrika ta Kudu, ka iya haifar da mace-mace sama da dubu 500,000 cikin shekaru goma masu zuwa.
Wannan na zuwa ne, bayan da attajirin nan na duniya mai fasahar ƙere-ƙere Elon Musk ya sanar da yanke duk wani agaji da Amurka ke bayar wa zuwa ƙasashen ketare, kodayake ya yi mi’ara koma baya game da tallafin yaƙi da cutar Ebola.
Musk ya bayyana wa taron muƙarraban gwamnatin Amurka cewa, ɓangaren gudanarwa na gwamnati ya yi kuskure bayan da ya ɗauki matakin sallamar wasu ma'aikata da kuma tsayar da wasu shirye-shirye a makwannin da suka gabata.
Elon Musk, wanda ba minista ba ne ko kuma wani zaɓaɓɓe a gwamnatin ta Amurka, ya ce ɗaya daga cikin kura-kuran, shi ne yanke agajin na yaƙi da cutar Ebola wanda ke ƙarƙashin USAID.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI