Amurka ta kashe jiga-jigan ƙungiyar Al-Shebab a Somalia

Amurka ta kashe jiga-jigan ƙungiyar Al-Shebab a Somalia

Babban kwamandan rundunar sojin Amurka a ƙasashen Afirka Africom ya tabbatar da kai harin a ranar talatar da ta gabata, cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai.

Sanarwa ta ce an kai harin ne da yawun gwamnatin Somalia inda aka kashe biyu daga cikin sanannun fuskoki kungiyar al-Shebab ba tare da raunata ko guda daga cikin fararen hula ba.

Ministan yada labarai da al’adun Somalia ya yaba da kisan jagoran mayaƙan jihadin Mohamed Mire da ake wa lakabi da Abu Abdirahman a wani rubutu da ya yi ta shafin sa na X.

Kungiyar al-Shebab wadda ke mubaya’a da ƙungiyar al-Qaida ta shafe sama da shekaru 15 ta na faɗa da gwamnatin Somalia da gwamnatocin ƙasa da ƙasa ke tallafawa.

A wa’adin mulkinsa na farko,  Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta kawo ƙarshen ayyukan sojin Amurka a Somalia, kafin wanda ya gaje shi wato Joe Biden ya soke matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)