Amurka ta kakabawa wasu kanfunan Rasha da China takunkumi

Amurka ta kakabawa wasu kanfunan Rasha da China takunkumi

Amurka ta yanke shawarar kakabawa wasu kamfanunnukan Rasha da China takunkumi a kan laifin siyarwa ma'aikatar harkokin makami mai linzamin kasar Iran kayayyaki.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa dangane ga hana shiga da magamai a kasashen Koriya ta Arewa, Iran da Siriya an bayyana kakkabawa wasu kanfunan Rasha da China takunkumi.

An zargi kanfuna biyu a ko wace kasashen biyu da laifin baiwa kanfanin fasahar makami mai linzami ta kasar Iran kayayyakin aiki.

An nemi kasashe da su guji duk wani yunƙuri da zai tallafawa ƙoƙarin bunkasa makami mai linzamin Iran.

Sanarwar ta kara da cewa za'a ci gaba da kakkabawa dukkanin kanfunan kasashen waje da ke baiwa ma'aikatar makamin linzamin Iran kayan aiki.

Takunkumin da aka kakkabawa kanfuna zai dauki tsawon shekaru biyu yan aiki.

 


News Source:   ()