Amurka ta harba tauraron dan adam mai leken asiri zuwa sama

Amurka ta harba tauraron dan adam mai leken asiri zuwa sama

Amurka ta harba wani tauraron dan adam mai leken asiri da ake kira "NROL-82" zuwa duniyar sama.

Tauraron na boye aiyukan da ya ke gudanarwa, kuma kamfanunnukan Lockheed Martin da Boeing ne suka hada hannu wajen samar da tauraron a kamfanin United Launch Alliance wanda aka harba shi a kumbon "Delta 4 Heavy"  ta Sansanin Jiragen Sama na Vandenberg da ke jihar California.

An yada harba tauraron kai tsaye ta yanar gizo.

 


News Source:   ()