Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka (Nasa) ta sanar da samar da bandaki da za'a yi amfani dashi dandamalin duniyar wata akan dala miliyan 23 (kimanin Naira Biliyan 10)
"yan saman jannatin hukumar NASA zasu dubu ko bandakin zai yiwu a iya amfani dashi a shirin zuwa duniyar watan dana maris da ake shirin yi.
Sabon bandaki da aka kashe dala miliyan 23 (kimanin naira biliyan 10) an bunkasashi yadda zai kasance daidai ga amfanin mata 'yan sama jannati.
Matukar dai 'yan sama jannatin suka amince da sahihancinsa za'a yi amafani dashi a balagurun zuwa duniyar wata da za'a yi a shekarar 2024.