Amurka ta fara bincike kan fitar bayanan sirrin shirin Isra'ila na kai hari Iran

Amurka ta fara bincike kan fitar bayanan sirrin shirin Isra'ila na kai hari Iran

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa ya samu gamsassun bayanai daga majiyoyi masu ƙarfi a rundunar Sojin Amurka da gwamnatin Sojin ƙasar da ke nuna cewa bayanan sahihai ne.

A cewar majiyoyin Iran ta raba bayanan yadda za ta kai harin ne ga ƙawayenta da suka ƙunshi Amurka da Birtaniya da Canada da New Zealand da kuma Australia, amma kuma aka samu fitarsu.

Majiyoyin sun shaidawa AP cewa yanzu haka Amurka na kan bincike don gano ta yadda bayanan suka fita, lamarin da ya wargaza shirin na Isra’ila.

Bayanan wanda aka bayyana da mafi ƙololuwar sirri, tun farko an wallafa su ne a shafin Telegram da Axios dukkanin jami’an gwamnatocin da abin ya shafa sun gaza amsa tambayoyin manema labarai game da bayanan.

Isra’ila wadda yanzu haka ke yaƙi a ƙasashen Lebanon da Falasɗinu da wani ɓangare na Syria ta sha alwashin mayar da martani kan Iran duk da yadda babbar ƙawarta kuma mataimakiyarta Amurka ta gargaɗeta game da mayar da martanin kan Tehran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)