Amurka ta cimma yarjejeniyar ma'adinai da Ukraine

Amurka ta cimma yarjejeniyar ma'adinai da Ukraine

Wani lokaci a yau Laraba ake sa ran a hukumance Ukraine za ta sanar da amincewa da yarjejeniyar haɗin gwiwar da za ta bunƙasa haƙowa da hada-hadar cinikayyar ma’adananta na ƙarƙashin ƙasa ciki har da man fetur da iskar gas.

Bayanai sun ce a ƙarƙashin yarjejeniyar, Amurka ta nemi mallakar wani kaso mai tsoka na ribar da za ta kai ta Dala Biliyan 500 daga ma’adanan ƙarƙashin ƙasar ta Ukraine.

Duk da cewa daftarin bai yi bayani ƙarara a kan batun samun tallafin ta fuskar tsaro daga Amurka ba, ministar shari’ar Ukraine Olha Stefanishyna, ta shaida wa Jaridar Financial Times cewa, yarjejeniyar za ta ƙunshi wasu ƙarin muhimman batutuwan da suka tattauna a kai, waɗanda Ukraine za ta amfana dasu.

A ranar Juma’ar da ke tafe ne kuma ake sa ran shugaba Volodimyr Zelenskyy zai yi tattaki zuwa Amurka don ganawa da da shugaba Trump, su kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar da wakilansu suka tattauna a kai.

Ukraine wadda ta malllaki ɗimbin arziƙin ma’adanan ƙarƙashin ƙasa da ake amfani da su a fannonin tsaro da samar da lantarki, baya ga man fetur da iskar gas, a nan gaba za ta riƙa zuba kaso 50 na ribar kuɗaɗen shigar da take samu daga garesu a cikin gidauniyar hadin gwiwar da za ta kafa da Amurka, inda daga cikin za a yi amfani da wani kaso wajen sake gina ƙasar ta Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)