Amurka ta ce Isra'ila ta amince da shawarwarin da ta bata na tsagaita wuta a Gaza

Amurka ta ce Isra'ila ta amince da shawarwarin da ta bata na tsagaita wuta a Gaza

Da yake jawabi sakataren harkokin wajen Amurka Antoni Blinken a ziyarar da ya kai Isra’ila, ya ce lokaci yayi da ya kamata Hamas ta amince da bayanan da ke cikin kundin don kawo karshen zubar da jinin mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Da yake zantawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala wani taro da manyan jami’an gwamnatin Isra’ila Antoni Blinken yace wannan yunkuri ka iya zama na karshe da zai dakatar da yakin da ke dosar shekara guda.

Bayanai sun nuna cewa zaman samar da maslaha ta karshe da aka gudanar a Qatar makon da ya gabata ya tashi ba tare da an cimma wata tartibiyar matsaya ba, sai dai ana sanya ran sake komawa a wannan makon karkashin biyayya ga shawarwarin da Amurka ta gabatar.

Ziyarar ta Blinken na zuwa ne dai-dai lokacin da Amurka ke cikin chukwu murdar siyasa wadda ke cin karo da zanga-zangar bangarorin da ke adawa da kuma goyon bayan ci gaba da yakin na Gaza.

Wannan yunkuri na zuwa ne dai-dai lokacin da adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarta dubu 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)